IQNA

Dan Kasar Iran Ya Zo Na Daya A Gasar Kur’ani Ta Duniya A Malaysia

23:24 - May 20, 2017
Lambar Labari: 3481531
Bangaren kasa da kasa, sakamakon karshe da aka sanar da gasar kur’ani ta 59 a kasar Malaysia Makaranci dan kasar Iran Hamed Alizadeh shi ne ya zo na daya.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga birnin Kuala Lumpur cewa, an kawo karshen gasar karatun kur’ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a kasar Malaysia, tare da halartar sarkin kasar.

A taron rufe gasar an sanar da sunayen wadanda suka fi nuna kwazo a dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar, inda Hamed Alizadeh daga kasar Iran ya zo na daya a bangaren karatun kur’ani mai tsarki, sai kuma wadanda suka zo a matsayi na biyu har zuwa biyar su ne; Haussain Taher Saker daga Iraki, Wan Fakhrurazi bin Wan Muhammad daga Malaysia, Muhamamd Ma’aruf Hussain daga Canada, sai kuma Nur Muhammad bin Ali daga Singapore.

A bangaren harda kuwa, kasashen Senegal, Qatar, Malaysia su ne suka zo a matsayi na daya da na biyu da kuma na uku kamar yadda aka ambata a jere, sai kuma bangaren mata da suka gudanar da harda, Najeriya ta zo na daya, sai Palastine ta biyu sai kuma Senegal ta uku.

Makaranta da mahardata 91 ne dai suka halarci gasar daga kasashe 49 na duniya.

A kalli bidiyon Karatun Hamed Alizadeh a nan.

3599530



Hamed Alizadeh


captcha