IQNA

Ministan Addini Na Masar:

Masu Hardar Kur’ani Suna Da Kwakwalwa A Sauran Karatuttuka

23:29 - May 20, 2017
Lambar Labari: 3481533
Bangaren kasa da kasa, minister mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa, ba abu ne mai yiwuwa ba mahardacin kur’ani a fadi a wani karatu na daban.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Aldastur cewa, Muhamad Mukhtar Juma’a minister mai kula da harkokin addini na kasar Masar ya bayyana cewa, wajibi ne a karfafa harkokin kur’ani mai tsarki ta dukkanin hanyoyi na koyarwa.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manyan malamai da limamai da kuma gwamnan jahar Daqhaliyyah a cikin wannan jaha, inda ya ce karfafa hanyoyin koyar da hardar kur’ani da aka gada iyaye da kakanni tana da muhimamnci.

Inda ya bayyana cewa babu wani wanda ya taba jin labarin cewa wani mahardaci ya kasa a wani fage na karatu, inda dukkanin masu hardar kur’ania duk inda ska shiga a wani fage na karatu to sukan yi zarra albarkacin hardar kur’ani mai tsarki.

Daga karshe ya kirayi dukkanin bangarori da cibiyo da suka kula da harkokin kr’ani a kasar da su kara mayar da hankali ga batun kyautata karatu da kuma harda, domin hakan shi ne zai kara shagaltar da matasa ga lamrin kur’ani, maimakon su koma suna bin wasu abubuwa da ba koyarwar muslunci ko al’adunsu ba.

Ya ce yanzu haka ana wani shiri na tura malamai guda 78 zuwa kasashen musulmi daban-daban, domin ganin yadda ake gudanar da ayyukan kur’ani, domin kara samun gogewa ta yadda zai zama malaman Masar suna da masaniya a kan salo daban-daban.

3601303


captcha