IQNA

Masarautar Bahrain Ta Yanke Hukunci A Kan sheikh Isa Kasim

19:19 - May 21, 2017
Lambar Labari: 3481534
Bangaren kasa da kasa, Kotun masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin shekara guda a kan babban malamin addinin muslunci na kasar Sheikh Isa Kasim.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin al'alam cewa, kotun masarautar ta yanke wannan hukunci ne a yau, duk kuwa da cewa shehin malamin baya a gaban kotun, domin kuwa dubun-dubatar al'ummar kasar suna ba shi kariya tare da hana jami'an tsaro isa yankin da yake.

Kotun ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan kaso a kan malamin, amma ba za a zartar da hukuncin ba har na da zuwa shekaru uku, kamar yadda kotun ta bayar da umarnin kwace dukkanin kudaden da suke a cikin asusun ajiyar na banki, da kuma cin sa tara da dinari dubu 100.

Tun kafin wannan lokacin dai masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta sanar da janye iznin zama dan kasa da kan malamin, bisa zargin cewa yana karbar kudaden zakka da khummusi ba tare da izinin masarautar ba, haka nan kuma yana goyon bayan masu adawar siyasa a kasar.

3601603


captcha