IQNA

Rawar Dan Kasuwa Mai Kyamar Muslunci Tare Da Iyayen Gidan Ta'addanci

19:23 - May 21, 2017
Lambar Labari: 3481535
Bangaren kasa da kasa, Donald Trump a zangon tafiyarsa ta farko bayan lashe zaben Amurka, ya fara da abokan kawancensa wajen aikin ta'addanci a duniya, da nufin hada karfi a tsakaninsu domin kalubalantar kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Asabar ne shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya a ziyararsa ta farko zuwa wata kasa ta waje tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar Amurkan.

Tun da fari dai shugaban Amurka wanda ya sami gagarumar tarba daga wajen sarkin Saudiyya Salman bn Abdul'aziz a jiyan sun sanya hannu kan yarjejeniyar cinikayya, cikikuwa har da ta makamai, da suka kai dalan Amurkan biliyan 380, inda biliyan 110 za su tafi ga bangaren makamai kawai, kana kuma a yau din nan Lahadi ne ake sa ran zai gana da wasu shugabannin kasashen larabawa da na musulmi inda zai musu karin bayani dangane da siyasar gwamnatinsa.

To sai dai abin tambaya a nan shi ne mai yasa shugaban Amurkan ya zabi Saudiyya a matsayin kasar farko da zai fara zuwa tun bayan darewarsa karagar mulki, Amsa wannan tambayar na bukatar yin karin bayani dangane da matsayin Saudiyya a wajen Amurka da kuma ci gaban siyasarta.

Ana iya dubi cikin muhimmancin Saudiyya ga Amurka ta bangarori da dama:

Na farko dai Saudiyya ita ce kasar ta farko wajen samar da man fetur a duniya wanda a kowace rana tana fitar kimanin ganga miliyan 10 na danyen man fetur wanda cikin hakan tana sayar da kimanin ganga miliyan bakwai duk da cewa Amurkan ba daga Saudiyyan take samun man da take bukata ba, to amma saboda irin matsayi da kuma tasirin da Saudiyyan take da shi wajen ayyana farashin man fetur a kasuwar duniya, don haka tana da matsayi na musamman wajen Amurkan.

Na biyu shi ne cewa Saudiyya tana daga cikin kasuwanni mafi girma da muhimmanci ga makaman Amurkan.

Don kuwa Saudiyya ita ce kasa mafi girma a duniya wajen sayen makamai, wanda wani bangare mai girman gaske na wadannan makamai daga Amurka take sayo su.

Rawar Dan Kasuwa Mai Kyamar Muslunci Tare Da Iyayen Gidan Ta'addanci

A saboda haka ne ma a yayin wannan ziyarar shugaban Amurka da Sarkin Saudiyyan suka sanya hannu kan yarjejeniyar sayen makaman Amurka da suka kai dala biliyan 110, wanda hakan zai share wa gwamnatin Trump din fagen karfafa tattalin arzikin kasar da ke cikin tsaka mai wuya da kuma ba shi damar cika wasu alkawurran da yayi wa Amurkan wajen kyautata tattalin arzikin kasar.

Na uku shi ne irin muhimmancin da Saudiyya take da shi a fagen siyasar Amurkan. Don kuwa ko shakka babu Amurka tana bukatar kasar Saudiyya wajen tabbatar da tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma karfafa matsayin da take da shi a yankin Gabas ta tsakiya, wanda hakan daya ne daga cikin manyan siyasar Amurkan, kamar yadda kuma Amurkan tana bukatar Saudiyya wajen cimma siyasarta a kasashen Iraki da Siriya.

Wani lamarin kuma a wannan fagen shi ne irin tarayyar da kasashen biyu (Amurka da Saudiyya) suka yi wajen kiyayya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran musamman a lokacin sarautar Sarki Salman din.

A saboda haka ne a halin yanzu kasar Saudiyya ta zamanto wani kayan aiki na biyan bukatun Amurka, na siyasa, tsaro, tattalin arziki da kuma al'adu a kokarin da Amurkan take yi na ci gaba da raunana kasashen musulmi da karfafa matsayin haramtacciyar kasar Isra'ila da tabbatar da tushenta a kasashen musulmi.

Rawar Dan Kasuwa Mai Kyamar Muslunci Tare Da Iyayen Gidan Ta'addanci

Wadannan suna daga cikin dalilan da da dama daga cikin masana suke ganin su ne suka sanya Donald Trump din sanya kasar Saudiyya a matsayin kasar farko da zai fara ziyarta.

To sai dai wani lamari da yake da muhimmanci a fahimta shi ne cewa, duk da wadannan dalilai da aka ambata, amma ko shakka babu dalolin man fetur din Saudiyyan su ne babban abin da Trump din yake kwadayi.

3601610


captcha