Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin zerohedge cewa, jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, akalla mutane ashirin da biyu suka rasa rayukansu a cikin sabon rikici da ya barke a arewa maso gabashin Jumhoriyar Afirka ta tsakiya.
Mataimakin Kwamandan Dakarun wanzar da zaman lafiya na majlaisar dinkin duniya a kasar Afirka ta Tsakiya diane corner a jiya Assabar na cewa fada tsakanin mayakan Saleka da na Anti Balaka a garin Bria na Jihar haute-Kotto dake arewa maso gabashin kasar yayi sanadiyar mutane ashirin da biyu tare da jikatta wasu sha bakawai na daban.
A yayin da yake bayyani kan wajibcin dakatar da wannan rikici, Mistan Diane Corner mataimakin Kwamandan Dakarun wanzar da zaman lafiya na majlaisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa fadace-fadacen da ya wakana cikin wannan maku da muke ciki yayi sanadiyar yin hijra na fararen hula kimanin dubu goma a garin Bria.
Tun a Shekarar dubu biyu d sha uku ne kasar Afirka ta tsakiyan ta fada cikin rikicin kabilanci da na addini, bayan juyin milkin da ya gudana a kasar, lamarin da ya janyo tsananin rashin tsaro tare da lakume rayukan mutane da dama.