IQNA

Wata Likita Daga Palastine Ta Zo Matsayi Na Biyu A Gasar Kur’ani Ta Malaysia

22:58 - May 22, 2017
Lambar Labari: 3481538
Bangaren kasa da kasa, wata likita mahardaciyar kur’ani mai tsarki mai suna Zainab Muhannid Hijawi daga Palastine ta zo a matsayi na biyu a gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a kasar Malysia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin labarai na Ramallah cewa, Zainab Saleh Muhannid Hijawi wata likita ce daga Palastine wadda ta hardace kur’ani mai tsarki, kuma ta samu nasarar zuwa a mataki na biyu a gasar kur’ani ta Malaysia.

Wannan bapalastiniya ta samu yabo daga jami’ai da kuma jakadan Palastine a Malaysia, inda aka shirya taro na musamman domin girmamata wanda ofishin jakadancin Palastinu ya dauki nauyin shiryawa.

Ta kammala karatu a bangaren likitanci, daga nan ta ci gaba da gudanar da ayyukanta kamar yadda da ta saba, tare da taimaka ma jama’a bangaren aikinta.

Haka nan kuma ta bayyana cewa, tun tana da shekaru 10 ne ta fara hardar kur’ani mai tsarki, a lokacin da ta kai shekaru 16 ta kammala hardar kur’ani baki daya.

Abin tuni a nan dai shine gasar Malaysia ta gudana ne a bangarori biyu da suka hada da bangaren mata da kuma bangaren maza, wanda kuma wannan shi ne karo na hamsin da tara da ake gudanar da wannan gasa.

Najeriya ce ce ta zo ta daya abangaren harda ta mata, sai kuma Palastine ta biyu, Senegal kuma ta zo a matsayi na uku a wannan gasa.

3602052


captcha