IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Rayuwar Imam Khomenei (RA) A Ghana

21:31 - May 23, 2017
Lambar Labari: 3481541
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taro kan rayuwar Imam Khomenei (RA) da yin dubi kan rubuce-rubucensa a a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren sadarwa na cibiyar yada al'adun muslunci ta kasar Iran cewa, nan da makonni biyu masu zuwa ne za a gudanar da tarukan cika shekaru 28 da rasuwar Imam Khomenei (RA) inda kuma za a yi taruka a kasashe daban-daban kan hakan, da hakan ya hada da birnin Accra na kasar Ghana.

Bayanin ya cea wannan taro za a gabatar da laccoci da bayanai a kan rayuwar Imam Khomenei (RA) da kuma irin abubuwan da ya bari na rubuce-rubuce a bangarori daban-daban na ilmomin addinin muslunci, tare da nuna littafansa kai tsayea wani baje koli na yanar gizo ta wannan adireshi : (www.aalyaseenghana.webs.com ) ga masu bukatar dubawa.

Baya ga haka kuma kuma akwai gasar da ake gudanarwa wadda daliban makarantu ne suke yin bincike kan rayuwarsa da kuma yin rubutu kan haka, inda za a karbi dukkanin abubuwan da suka rubuta tare da bas u kyautuka na musamman a kan hakan.

3602596

captcha