IQNA

Abubuwan Da Ziyarar Trump Ta Kunsa Na Karo Da Juna

23:12 - May 24, 2017
Lambar Labari: 3481545
Bangaren kasa da kasa, bayan gama ziyarar da ya kai a birnin Riyadh fadar masarautar Saudiyya, tare da gabatar da jawabi ga wasu shugabannin larabawa da na wasu kasashen musulmi, Donald Trump kai tsaye ya wuce zuwa Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ziyarar tasa a Isra'ila ba ta da wani banbamci da wadda ya kai a Saudiyya a siyasance, domin kuwa tana a matsayin ci gaba ne na abin da suka cimma matsaya a kansa tare da sarakunan Saudiyya, wato hada karfi da karfe a tsakaninsu domin yaki da Iran, inda bayan isarsa Isra'ila, Trump ya tabbatar da cewa wannan kawance ne na Amurka da Saudiyya da Isra'ila domin yaki da kasar Iran, wadda ta zama babban karfen kafa da ke kawo tarnaki ga manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya.

Tun da Trump ya saka kafarsa a cikin Saudiyya dai har ya bar kasar bai yi magana a kan mulkin dimukradiyya ko kare hakkokin bil adama ba, kamar yadda bai yi maganar harin 11 ga watan Satumba da aka kaiwa Amurka ba, haka nan kuma bai yi magana a kan kawo karshen zaluncin da Palastinawa suke fuskanta a hannun yahudawan Isra'ila ko kuma wajabcin kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta

Masan da dama suna ganin cewa, babbar manufar wannan yawo da Trump ke yi a gabas ta tsakiya dai ita ce tabbatar da tsaron yahudawan Isra'ila, domin kuwa kada kugen yakin da ya yi a kan Iran daga birnin Riyadh ba manufarsa kare Saudiyya ko wata kasa daga cikin kasashen larabawa ba ne, manufar ita ce kare Isra'ila wadda a kullum take kallon Iran a matsayin babbar barazana a gare ta, kamar yadda hatta makudan kudaden da Amurka take karba daga hannun Saudiyya da wasu larabawan yankin.

Mafi yawan wadannan kudaden za su tafi ne wajen karfafa tsaron Isra'ila da kuma kara danne al'ummar Palastinu marassa kariya, kamar yadda kuma wasu daga cikin makaman da wadannan gwamnatocin kasashen larabawa suke saye na biliyoyin daloli daga Amurka, suna tafiya ne a hannun kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kuniyoyin da ake amfani da su wajen hare-haren ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen larabawa irin su Syria da Iraki da Libya da sunan jihadi, kamar yadda kuma wasu daga cikin makaman da Saudiyya ta kulla cinikin sayen su daga Amurka yayin ziyarar Trump a Riyadh, Saudiyya za ta yi amfani da su ne wajen kai hare-hare a kan al'ummar musulmi larabawa na kasar Yemen.

To sai dai wani abu da masana harkokin siyasa na duniya suka yi imani da shi, shi ne cewa, dukkanin kasashen larabawan da Amurka take amfani da su domin cimma manufofinta ayankin gabas ta tsakiya, magana ce kawai ta lokacin da Amurka take da maslaha da su, da zaran maslarta ta kare, tabbas za ta yi watsin shara da su, kamar yadda ta yi hakan a kan takwarorinsu da dama suka gabata

3602673


captcha