Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daruruwan motoci masu sulke na jami'an tsaro tare da daruruwan 'yan banga na masarautar kama karya ta Al Khalifa, suna ci gaba da killace gidan Ayatollah Sheikh Isa Kasim, bayan da suka kashe wasu daga cikin masu zaman dirshan a wurin, da kuma jikkata daruruwa, da kuma kame wasu daruruwan na daban
Har yanzu dai babu wani wanda ya san halin da malamin yake ciki, kamar hatta iyalansa ba su san inda yake ba, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suke ci gaba da yin tir da Allah wadai da wannan mummunan aiki na masarautar kasar.
Masarautar bahrain dai tana zargin Sheikh Isa Kasim da karbar kudaden zakka da Khumusi da mabiyansa ke aika masa da su ba tare da ya karbi izinin yin hakan daga masarautar ba, ida masarautar ta bayyana hakan a matsayin halasta kudaden haram.