IQNA

Za A Dauki Azumi A Ranar Asabar A Mafi Yawan Kasashe

23:45 - May 25, 2017
Lambar Labari: 3481549
Bangaren kasa da kasa, a ranar Asabar mai zuwa ce a ke sa ran za a dauki azumin watan Ramadan a mafi yawan kasashen musulmi na duniya

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Almuwatin cewa, ranar 26 ga watan Mayu 29 ga Sha'aban kasashen msuulmi da dam aba za su iya ganin watan azumi da idanu ba.

Amma za a iya ganin watana wasu kasashen kudancin Amurka da kuma wasu yankunan nahiyar Afirka, kamar Sudan, Mauritaniya, Morocco, Somalia da kuma Aljeriya.

Haka nan kuma bayanin ya nuna cewa, da wuya a iya ganin jinjirin watan a cikin kasashen larabawa da kuma yankin gabashin nahiyar Asia.

Bisa ga wannan bayani, mafi yawan kasashen musulmi za su fara azumi aranar asabar mai zuwa, kamar yadda kuma hakan zai zama daya cikin lokuta da za a fara azumi kusan duk lokaci guda atsakanin kasashen musulmi.

A bangare guda ofishin babban malamin addini a Iraki Ayatollah Sayyid Sistani ya sanar da cewa, ranar Juma'a babu tabbacin cewa za ta zama cikin raman, saboda haka sai jama'a su yi kamun baki a ranar.

3602776


captcha