IQNA

Gasar Hardar Kur’ani Wadda Ta Kebanci ‘ya’yan Lauyoyi A Masar

23:29 - May 26, 2017
Lambar Labari: 3481551
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki wadda ta kebanci ‘ya’yan lauyoyi a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na sal balad ya bayar da rahoton cewa, ana shirin fara gasar hardar kur’ani mai tsarki wadda ta kebanci ‘ya’yan lauyoyi zalla a kasar Masar.

Wannan gasa dai zata gudana ne babban dakin taruka na Alnahri da ke yankin Almu’adia cikin birnin Alkahira.

Hassan Abu Isa babban sakataren kungiyar lauyoyi ta kasa ya bayyana cewa, an shirya wannan gasar ne domin kara jawo hankulan ‘ya’yan lauyoyi zuwa ga sha’anin kur’ani mai tsarki da kuma karfafa gwiwarsu a kan hardarsa.

Ya ce an riga an bayyana yadda gasar za ta gudana acikin bayanin da ke cikin fam din rijista, kuma tuni aka samu wadada za su shiga gasar sun kammala bayar da abubuwan da ake bukata.

Za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa ranar 26 ga watan Ramadan mai alfarma.

3603325


captcha