IQNA

Musulmin Sweden Sun Yi Allah Wwadai A Kan Gaisawar Sarkin Saudiya Da Matar Trump

23:34 - May 26, 2017
Lambar Labari: 3481553
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Sweden sun yi tir da Allah wadai da gaisawar da sarkin Saudiyya ya yi da matar shugaban Amurka Donald Trump.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, musulmin kasar Swden a shafuka daban-daban na zumunta da yanar gizo sun yi ta nuna bacin ransu da yin tir da Allawadai da gaisawar da sarkin saudiyya Salman bin Abdulaziz ya yi da matar Donald Trump.

A cikin wani shafin yanar gizo na msuulmin kasar Sweden mai suna Islamisket, musulmin sun bayyana abin da sarkin na masarautar Saudiyya ya yi na gaisawa da matar Trump wadda ba muharramarsa ba, hakan ya yi hannun riga da koyarwar addinin muslunci, hakan yana matsayin babban sabon Allah wanda ya haramta.

Wannan bayani ya samu goyon bayan mutane da dama da suke shiga shafin, wadanda akasarinsu musulmin kasar ta Sweden ne, wadanda suke ganin hakika wannan aiki ya yi hannun riga da koyarwar sunnar manzon Allah.

Yayin da wasu kuma daga cikin masu bayyana ra’ayinsu a kan wannan bayani suke yin Karin haske da cewa, hakan ba cin mutunci ne kawai ga Saudiyyah ba, cin mutunci ne ga muslucni da kuma musulmi baki daya, domin kuwa Saudiyya musulmi da yawa sun dauka ita ce ke wakiltar musulmi baki daya,a lokacin da sarakunanta suka zubar da kimar kansu da addininsu su zubar da kimar musulmi ne baki daya.

A cikin shekara ta 2015 Donald Trump ya soki Michel Obama saboda zuwa saudiyya da ta yi ba tare da dan kwali a kanta ba.

3603277


captcha