Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin The News cewa, a kowace shekara musulmi mazauna birnin quds suna raya watan Ramadan mai alfarma ta hanyar gubatar da shirye-shirye da suka shafi kur’ania masallacin aqsa.
Assam Zigair wani mai shago ne dan shekaru 67 da haihuwa, wanda yake sayar da fitilu da ake amfani da su a cikin watan Ramadan bisa aladar larabawa, inda ya kai kai fitilun da yake sana’antawa zuwa kasashen da suke makwaftaka da Pakastine.
Baya ga haka mazauna wannan birnin suna kayata dukkanin hanyoyi da lunguna domin murnar watan Ramadan mai alfarma, inda akan yi tarukan cin abincin buda baki na bai daya a dukkanin yankna na birnin mai alfarma.
Haramtacciyar kasar Isra’ila takan dauki tsauraran matakai na hana palastinawa gudanar da tarukansu da suka saba yi a cikin azumin watan Ramadan, amma duk da hakan sukan yi abin da ya sawaka, kamar yadda suka yi tarukan karatun kur’ani mai tsarki a cikin masallacin qasa.