IQNA

An Gano Wani Bangare Na Jirgin Annabu Nuhu (AS)

23:46 - May 27, 2017
1
Lambar Labari: 3481555
Bangaren kasa da kasa, wasu masana masu bincike akan kayan tarihi sun gano wani katako da ake zaton yana da alaka da jirgin annabi Nuhu (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Almanar cewa, wasu masana Turkawa da kuma ‘yan China sun gano wani katako da ake ganin yana daga cikin bangaren jirgin ruwan da annabi Nuhu ya sassaka.

Wadannan masana sun gano wannan katako a kan tsaunin Ararat mai tsawon mita 4,500, duk kuwa da cewa kankara da kuma aman wuta sun rufe wannan katako, amma dai an iya gani cewa yana da alaka da zamanin annbin Nuhu, kimanin shekaru 4,800 da suka gabata.

Masanan suna cewa zato kashi 99.9 cikin dari na nuni da cewa wannan katako yana da alaka da jirgin annabi Nuhu (AS).

Ayoyin kur’ani mai tsarki sun yi ishara da wannan jirgi, daga ciki akwaii aya ta 27 a cikin surat Muminun, da ke bayar da kissar annabi Nuhu(AS) kan cewa Allah madaukakin sarki ya uarce da yak era jirgin ruwa, bayan nan kuma aka umarce da ya dauki jinsin namiji da mace na dukkanin halite guda biyu-biyu,a haka Allah ya tseratar da shi da muminai.

3603360


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
7
9
ALLAHU AKBAR
captcha