IQNA

Hanyoyi Uku Na Jan Hankalin Yaro Zuwa Ga Karatun Kur’ani

23:47 - May 29, 2017
Lambar Labari: 3481562
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin masana ilimin halayyar dan adama kasar Masar ta yi bayani kan wasu hanyoyi da za su iya taimakawa wajen hankalin yaro zuwa ga kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na alhyatalmasrya cewa, watan Ramadan wata ne da musulmi musamman iyaye mata suke amfani da shi wajen jawo hankulan yaransu zuwa ga kur’ani mai tsarki.

Muna Yusri, kwararra ce a kan ilimin sanin halayyar dan adam, ta kuma bayyana wasu hanyoyi guda uku wadanda suke da tasiri wajen jawo hankulan yara zuwa lamarin kur’ani da hakan ya hada da karatunsa har da harda.

Hanyoyin su ne kamar haka:

1 – Yin karatu a bayyane a gaban yaro da sauti mai dadi mai kwantar da hankali, ta yadda zai zauna da kansa yana sauraron abin da ake karantawa.

2 – Nuna tasirin abin da ake karantawa a gaban yaro, tare da yi masa bayani a cikin hikima a kana bin da kur’ani ko kuma wasu daga cikin ayoyi suke cewa.

3 – samar da kayan wasa ga yaro wadanda suke dauke da sauti na karatun ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda hakan zai taimaka masa wajen rike ayoyin da ake karanwa da kuma yadda ake karanta su, bugu da kari kuma zai hardace ayoyin da yake ji ana karantawa cikin sauri.

3603964


captcha