IQNA

Firayi Ministan Indiya: Ramadan Wata Ne Na Aminci, Rahma, Da Kaunar Juna

23:50 - May 29, 2017
Lambar Labari: 3481563
Bangaren kasa da kasa, Prime ministan kasar India Narendra Modi ya bayyana watan Ramadan a matsayin watan zaman lafiya da rahma da kara fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar India.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar The News ta kasar India ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da ya aike wa dukkanin musulmin kasar India domin taya su murnar shiga watan azumin Ramadan mai alfarma, firayi ministan India ya bayyana farin cikinsa a kan abin da ya kira muhimmancin da watan ramadan yake da shi wajen kara hada kan al'ummar India.

Ya ce yana fatan dukkanin al'ummar musulmi na Inidia da ma na duniya baki daya za su yi azumin watan Ramadan cikin koshin lafiya, kamar yadda kuma ya yi fatan wanann wata ya zama sanadin na kara samun kwanciyar hankali a kasashen musulmi da na duniya baki daya.

A kasar India akwai musulmi da yawansu ya kai muliyan 180, inda kasar take a matsayin kasa ta uku a duniya wajen yawan musulmi, bayan Indonesia da Pakistan.

3604139


captcha