IQNA

Gasar Kur'ani Ta Watan Ramadan A Cibiyar Azhar

17:22 - May 30, 2017
Lambar Labari: 3481564
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar kur'ani ta watan Ramadan a karkashin kulawar cibiyar Azhar.

Kamfannin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin jaridar Al-dastur cewa, wannan gasa ta kunshi kyauwun sauti da kuma harda.

Babban malamin cibiyar Azhar ne ke kula da wannan gasa tare Muhammad abdulsamad Mahna babban limamin cibiyar.

Gasar dai za a fara ta ne daga gobe, kuma za a gudanar da ita ne kai tsaye daga cikin masallacin cibiyar Azhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin Masar.

Kamar kowace shekara a kan bayar da dama ga masu bukatar shiga gasar da su yi rjistar sunayensu, inda akan samu mutane daga sassa daban-daban na asar da suke shiga wannan gasa.

Daga cikin wadanda suke shiga gasar akwai daliban cibiyar ta Azhar wadanda yan asalin kasar Masar ne, kamar yadda kuma akwai wasu yan kasahen ketare da suke karatu a wurin, da kuma mazauna cikin gari.

Daga karshe akan bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazoa wanann gasa.

3604692
captcha