IQNA

Adadin Musulmi Zai Karu A Amurka A Shekara 2050

17:24 - May 30, 2017
Lambar Labari: 3481565
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon wani bincike da wata cibiyar kididdiga ta gudanar a kasar Amurka, ya nuna cewa adadin musulmi a kasar ta Amurka zai kai karu da kashi saba'in cikin dari a cikin shekara ta dubu biyi da sattin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na lifezette ya habarta cewa, cibiyar PIo da ke gudanar da ayyukan kididdiga ta fitar da wasu alkalumma da ke nuni da cewa adadin msuulmi zai kai karu da kashi 70 cikin dari a shekara 2016.

Rahoton ciyar ya ce addinin muslunci ya fi saurin yaduwa fiye da addinan kiristanci da kuma Hindus, wadanda su ne suka fi yawa a kasar Amurka, inda muslunci yake a matsayin addini na uku wajen yawan mabiya akasar bayan kiristanci da Hindus.

Haka nan kuma rahoton ya yi nuni da cewa, baya ga shiga addinin muslunci da wasu mabiya addinai suke yanayin tsarin iyali na musulmi na taka rawa wajen karuwar musulmi a duniya.

Rahoton ya ce karuwar musulmi ta hanyar shiga muslunci ko kuma haihuwar da musulmi suke yi a cikin nahiyar turai, a shekara ta 2050, msuulmi za su zama kashi 10 cikin dari na dukkanin al'ummar nahiyar turai.

3604752

captcha