IQNA

Taro Kan Kan Adalcin Zamantakewa A Mahangar Imam Khomeini A Indonesia

22:09 - May 31, 2017
Lambar Labari: 3481567
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zama a kan mahangar Imam Khomeinidangane da adalcin zamankewa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin yada al'adun muslunci na Iran a kasar Indonesia tare da jami'an Sharif Hidayatollah Jakarta UIM za su dauki nauyin shirya zaman taron karawa juna sani a kan adalcin zamantakewa a mahangar marigayi Imam Khomeini.

Taron dai zai gudana ne a ranar laraba mai zuwa, inda masana da malamai za su gabatar da jawabai da makaloli a kan wannan maudu'i, daga cikinsu kuwa har da Rumadi Ahmad, fitaccen masani kan harkokin addini a kasar kuma malami a wanann jami'a, da kuma jakadan Iran a kasar Waliyullah Muhammadi Nasr Abadi.

Wanann taro dai zai samu halartar manyan malamai na sunna da kuma na shi'a gami da masana da suka hada da malamaan jami'oi, inda za su bayyana mahangarsu a kan yadda Imam Khomeini yake kallon adalci a rayuwar zamantakewa, daga irin abubuwan da ya bayya a acikin littafan da ya rubuta awannan fage.

Jami'ar Sharif Jakarta UIM dai tana daga cikin muhimman jami'oin kasar Indonesia, wadda aka gina a cikin shekara ta 1957, kuma tan ada dalibai dubu 23 a halin yanzu da suke karatu.

3605240


captcha