IQNA

Masu Addinin Maguzanci Su 300 Sun Musulunta A Najeriya

22:12 - May 31, 2017
Lambar Labari: 3481568
Bangaren kasa da kasa, Wasu daga cikin masu addinin maguzanci sun karbi addinin muslunci a a cikin jahar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, mutanen sun karbi addinin muslucni ne a cikin wannan wata na Radan mai alfarma a cikin kananan hukumomin Funtua da Bakori da ke kudancin jahar.

Sheikh Salisu Bakori shi ne shugaban kwamitin da ke kula da ayyukan isar da sakon muslunci ga masu bin addinin maguzanci a cikin jahar Katsina, ya bayyana cewa sakamakon kokari da malamai suke yi na fahimtar da Hausawa masu bin addinin maguzanci, an samu mutane 300 daga yankuna 27, na jahar.

Ya ce babbar matsalar da ake fuskanta a bangaren isar da sakon musulunci ga maguzawa ita ce, malamai suna yin kasa a gwiwa matuka a wannan bangare, wanda hakan ne ya sanya wasu da dama daga cikinsu suke shiga addinin kirista, saboda rashin samun wani bayani a kan addinin muslunci.

3605145


captcha