Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin Metro News cewa, musulmi a kasar Canada suna tara taimako domin taimaka ma marassa karfi a wasu kasashen ketare.
Wannan taimako dai an fara tattara shi ne da nufin aikewa da shi zuwa ga al’ummar Somalia, amma daga bisani ana tunanin fadada lamarin har zuwa ga wasu kasashen da suke fama da matsaloli na rashi.
Farhin Khan shi ne babban darakta mai kula da harkokin kungiyar da ke gudanar da wadannan ayyuka kan lamurran da suka shafi kasashen ketare, ya kuma bayyana cewa wannan shiri yana samun karbuwa fiye da yadda aka yi zato.
Y ace akwai mutane kimanin miliyan 30 da suke fama da matsalar yunwa ahalin yanzu a kasashe daban-daban da suke bukatar taimakon gaggawa, akan haka wannan taimako zai isa ga al’ummar Somalia daga farko, amma kuma za a ci gaba da fadada aikin taimakon zuwa ga wasu mabukata a wasu kasashen.
Dukkanin wadanda suke gudanar da wanbnan aiki dai suna yi ne domin kashin kansu, ba tare da wani ya sanya sub a, kamar yadda kuma babau wata lada da ske karba a kan hakan.