IQNA

Bayar Da Horo Kan Kur'ani A Afirka Ta Kudu

23:50 - June 03, 2017
Lambar Labari: 3481578
Bangaren kasa da kasa, ofishin kula da harkokin yada al'adun muslunci na kasar Iran a Afirka ta kudu ya dauki nauyin shirya wa dalibai musulmi tarukan bayar da horon a kan kur'ani a cikin watan Ramadan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ofishin kula da yada al'adun muslunci na Iran a kasar Afirka ta kudu ya sanar da fara gudanar da wani shiri na bayar da horar ga dalibai musulmi kan kur'ani mai tsarki.

Shugaban ofishin Ibrahim Butshakan ya bayyana cewa, wannan shiri an fara shi ne daga wannan shekara a garin Winterfield na kasar Afirka ta kudu, inda dalibai dari da sattin dukkanin musulmi da suke karatu a makarantun sakandare, suke samun wannan horo.

Horon wanda Iran take daukar nauyinsa, malamai na makarantun cibiyoyin musulmin kasar Afirka ta kudu suke jagorantarsa, daga cikin abubuwan da ake gudanrwa kuwa har da tsarin karatun kur'ani tare da sanin hukunce-hukuncensa, da kuma gabatar da laccoci na muslunci da suka hada da kissoshin kur'ani.

Daga karshe kuma za a gudanar da jarabawa ta musamman a an dukkanin abubuwan da ak agudanar, inda za a bayar da kyauta ta bai daya ga dukkanin daliban da suka halarci horon, haka nan kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3606240


captcha