Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na jaridar Alqabs ta Kuwait ya bayar da rahoton cewa, Abdulmutallab Sari Kaya dan shekaru 67 an haife shi ne a garin Manisa.
An haife shi a matsayin makaho kuma ya koyi karatun kur’ani ne tun yana dan shekaru 10 da haihuwa, amma daga bisani kuma ya hardace kur’ani baki daya.
Daga bisani yay a rika yin karatun kur’ani mai tsarki a masallacin manisa a kowane watan azumin Ramadan, inda yak an karanta izihi biyu a kowace ranara, jama’a suna zaune suna sarara, ya kammala karatun kur’ani iazihi sattin a daren sallah.
Yanzu shekaru 44 kenan a jere wanan mutum da Allah yay i wa wannan babbar baiwa yana gudanar da wannan aiki.