IQNA

Musulmi A Teesside Na Bayar Da Buda Baki Ga wadanda Ba Musulmi ba

23:55 - June 18, 2017
Lambar Labari: 3481621
Bangaren kasa da kasa, musulmi a birnin Teesside na kasar Birtaniya suna bayar da abincin buda baki ga wadanda ba musulmi ba da nufin karfafa fahimtar juna a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na gazettelive cewa, musulmin sun shirya buda bakin ne a babban masallacin na birnin Teesside.

Wannan masallaci dai yana daga cikin masallatai mafi girma akasar Birtaniya da ke daukar masallata 2500 a lokaci guda, wanda kuma ya dauki tsawon shekaru 12 ana gina shi, a kan kudade da suka kai fan miliyan 2.2.

Musulmin birnin na Teesside sun gayyaci sauran jama’a wadanda ba musulmi zuwa masallacin domin yin buda baki tare da su da kuma duba irin ayyukan da musulmi suke gudanarwa a wurin.

Shakil Hussain shi ne mai kula da ayyukan masallacin ya bayyana cewa, wannan mataki yana da tasiri matuka, musamman ganin cewa a duk lokacin da aka yi irin wannan kira wasu daga cikin mutanen Birtaniya da ba su adawa da musulunci suna halartar wurin, tare da nuna farin cikinsu.

Ya kara da cewa babbar manufarsu a kan shirya wannan buda baki dai ita ce kara kusanto da fahimtar juna da kuma samun zaman lafiya a tsakanin musulmi da sauran mabiya addinai.

3610848


captcha