IQNA

Musulmin Los Angeles Na Taimaka Ma Marassa Karfi

23:57 - June 18, 2017
Lambar Labari: 3481622
Bangaren kas da kasa, musulmi masu azumi suna taimaka ma mutanen Los Angele marassa karfi da kayyakin bukatar rayuwa a cikin wannan wata mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, musulmin na birnin Los Angeles suna gudanar da wannan aiki a kowace shekara, domin isar da sakon zaman lafiya da ‘yan adamtaka ga sauran mutane da ba musulmi kamar yadda addinin muslunci ya koyar.

Daga cikina bubuwan da suke bayarwa akwai abinci, kayan kiwon lafiya da suka hada da salullai da sauransu, da kuma tufafi gami da kayan karatu na makaranta da suka hada da littafai da jikkuna da sauransu.

Uamr Hakim shi ne shugaban wannan cibiya ta msuulmi da take gudanar da wadannan ayyuka na alhairi a birnin na Los Angele ya bayyana cewa, su Amuekawa ne msuulmi, kuma suna gudanar da wannan aiki na taimaka ma sauran Amurka wadanda ba msuulmi ba kamar yadda muslunci ya yi umarni da a taimaki mai bukatar taimako.

Birnin Los Angele dai na daga cikin biranan da musulmi suke fuskantar matsaloli na zamantakewa, sakamakon kyamar da ake nuna wa musulmi, musamman bayan da Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar.

3610756


captcha