IQNA

Jagora Yayin Ganawa Da Fira Ministan Iraki:

Kada Ku Taba Amincewa Da Amurka Suna Jiran Dama Ne Domin Su Yake Ku

23:46 - June 20, 2017
Lambar Labari: 3481626
Bangaren siyasa, a lokacin da yake ganawa da firayi ministan kasar Iraki Haidar Ibadi a yau, jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei (DZ) ya yi nasiha ga firayi ministan na Iraki da cewa, kada ku taba amincewa da Amurka domin kuwa a kowane koaci za ta iya cutar da ku.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yau yayin ganawar jagoran da kum afirayi ministan na Iraki, an duba batutuwa daban-daban da suka shafi matsalolin da aka haifar a yankin gabas ta tsakiya da nfin tarwatsa al’ummomin yankindomin Amurka da yahudwa su karensu babau babbaka.

Jagora ya yi nasihohi ga bangaren Iraki da cewa ya kamata su gaba da zama tsintsiya daya madaurinki daya, kada su taba yarda da duk wani abin da zai kawo rarraba a tsakanin al’ummar Iraki a dukkanin bangarori, na mazhaba ko kabila ko ma addini.

A yayin da yake jinjinawa hakin kan da aka samu tsakanin 'yan siyasa da maliman addinin kasar Iraki wajen yaki da Kungiyar ISIS, Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khamenei, ya yaba da rawan da Dakarun Al'umma suka taka a yaki da Kungiyar IS.

Jagora ya ce Jumhoriyar musulinci ta Iran a matsayin ta na makwabciyar kasar Iraki tana adawa da duk raderadin cewa a gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a na ballewar wani bangaren kasar, duk masu wannan gunaguni makiyan kasar Iraki ne.

Yayin da yake tabbaci a kan hadin kan Al'ummar kasar Iraki da kuma kiyaye kasar, Jagora ya ce ya zama wajibi Al'ummar kasar su zamanto masu basira dangane da makircin kasar Amurka, kadda su taba amincewa da Amurka saboda da ita tana adawa da kasancewar kasar Irakin a matsayin dunkulaliyar kasa guda.

Yayin da yake bayyani dangane da adawar da magabatan Amurka suka nuna na shigar Dakarun sai kai na Al'ummar kasar wato Hashadu Sha'abi cikin yaki da kungiyar Ta'addancin IS da ta mamaye wani bangaren kasar a shekarun baya, Jagoran juyin juya halin musulinci ya ce dalilinsu na yin haka shi ne fargabar da suke da shi na rasa matsayin da suke da shi a kasar

Jagora ya kara jadadda cewa ko da wasa kada ku amince da Amurka saboda a ko wani lokaci tana jiran dama ce na yin tasiri da kuma samun wuri a cikin kasa ne.

3611655


captcha