IQNA

Shugaban Kenya Ya Rabawa Musulmi Dabinon Buda Baki

23:52 - June 21, 2017
Lambar Labari: 3481629
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Kennya Uhuru Kenyatta ya rabawa musulmi mabukata dabinon buda baki wanda ya kai Ton 36.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta daga birnin Nairobi cewa, shugaban kasar ta Kenya da kansa ne ya tanadi wannan dabino domin raba shi ga musulmi mabukata a cikin wanann wata mai alfarma.

Uhuru Kenyatta ya bayar da dabinon ga kungiyoyin musulmi domin su raba shi ga mabukata daga cikin musulmi a cikin wannan wata, bayan ganawar da ya yi da su a fadarsa.

Kenyatta ya bayyana wanann wata amatsayin taimako da jin kai ga mabukata, kuma nauyi ne da ya rataya akan kowa da ya taimaka ma mai karamin karfi, domin a samu yaduwar albarka a tsakanin al'umma.

Kungiyoyin musulmi sun karbi wannan dabino wanda tuni aka far araba shi ga mabukata a yankuna daban-daban na kasar, lamarin ya da kara karfafa fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar wadda akasarin su abiya addinin kirista, amma wannan aiki da shugaban kasar ya yi wanda shi ma kirista ne, ya sanya da dama daga cikin mutane suna jin jina masa.

A lokutan baya dai masu dauke da akidar wahabiyanci da suka kaddamar da hare-haren ta'addanci, sun yi ta kai hare-hare na kisan jama'a musamman kiristoci a kasar ta Kenya, lamarin da ya kawo rashin fahimta da kuma tsangwamar musulmi musammana birnin Nairobi da wasu yankunan kasar.

3611976


captcha