IQNA

Hotuna Daga Masallacin Khalifancin Daesh Da Aka Rusa

22:32 - June 22, 2017
Lambar Labari: 3481633
Bangaren kasa da kasa, an nuna hotunan daya daga cikin tsoffin masallatan tarihi da aka rusa a jiya wanda ‘yan ta’addan daesh suka mamaye suka mayar da shi a matsayin wurin abin da suke kira khalifancin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar nbcnews cewa, Rundinar sojin Iraki ta ce kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta wargaza masallacin Al-Nouri da kuma hasumiyar Mosul mai dadadden tarihi.

Fira ministan Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wargaza wadanan wurare ya nuna cew an yi galaba ne ga yakin da ake da kungiyar IS.

Saidai a wata sanarwa data fitar ta hanyar shafin yada farfagandanta na amaq,kungiyar ta IS ta musunta wargaza wuraren tana mai dora alhakin hakan ga jiragen yakin Amurka.

Amman kawancen yaki da 'yan ta'addan naIS ya ce kungiyar ta wargaza daya daga cikin mayan wurare masu tarihi na Mosul da Iraki.

Idan ana tune amasallacin na Al-Nourine dake MosulAbou Bakr al-Baghdadi ya ayyana kansa a matsayin Khafika bayan da kungiyar ta IS ta mamaye yankin a cikinshekara dubu biyu da hudu.

3612222


captcha