IQNA

An Gano Wasu Kofai Na Musulunci A Adis Ababa

22:42 - June 25, 2017
Lambar Labari: 3481642
Bangaren kasa da kasa, wasu masu gudanar da bincike a kan wuraren tarihi sun gano wani gari a kusa da birnin Ais Ababa na kasar Habasha da ke da alaka da musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar Independent ta bayar da rahoton cewa, masu gudanar da bincikn sun ce wurin yan adauke da wasu abubuwa na tarihi wadanda suke da alakada da kasashen musulmi kuma tarihinsu yana komawa zuwa ga shekaru fiye da dari bakawai a wani wani gari wanda ya shafe kuma aka sake tono shi.

Daga cikin abubuwan da aka samu akwai tsoffin karau da kuma wuri gami marmar da gilassai wadanda msuulmi suke amfani da su daga kasashen Madagaska da Maldiv Yemen da kuma China.

Timosy Insel daga kasar Birtaniya masani ne a kan gano abubuwan tarihi ya bayyana cewa, akwai wani wurin kasuwanci da kuma masallatai da wasu ciciyoyi da aka samu a wurin, sun kama da ginin masallatan Tazania da kuma Somalia.

Ya ce ganin wadannan abubuwa ya sanya sun kara samun tabbaci a kan cewa hakika wurin yana da alaka da musulmi, baya ga haka kuma sun samu kudade na zinari da azufa ga kuma tagwalla, wadanda aka yi musu zane da ke nuna alama ta musulunci.

Yanzu haka dai an dukufa wajen gudanar da bicnike a kan wadannan abubuwa domin kara samun tabbacia kansu da kuma tarhinsu.

Kasar Habasha dai tan adaga cikin kasashen nahiyar Afirka da suka fara samun mutanen da suka fara karbar addinin muslunci tun daga lokacin zuwan musulunci ba da jimawa ba.

3613189


captcha