IQNA

Gasar Rubtu Kan Imam Khomeni (RA) A Uganda

23:51 - July 08, 2017
Lambar Labari: 3481680
Bangaren kasa da kasa, an shirya wata gasar rubtu kan rayuwar Imam Khomeni (RA) a kasar Uganda wadda ofishin kula da harkokin al’adun muslunci ya shirya.

Kamfanin dillancin labara iqna ya bayar da rahoton cewa, an shirya wannan gasane da nufin bayar da dama ga mutanen kasar Uganda su samu masaniyya a kan ImamKhomeni (RA) ta hanyar bincike da kuma irin gagarumin aikin da ya yi alokacin rayuwarsa.

An daga lokacin karbar wannan rbutu daga aka sanya kwanaki 15 zuwa wata, domin bayar da dama ga masu rubutun su samun lokacin bincike da suke bukata.

Ofishin kula da al’adun musulunci na kasa Iran da ke Uganda ne ya dauki nauyin shirya wannan gasa, kuma zai bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka zo na fako harzwa na uku da na hudu.

Daga cikin wadanda suka mika abubuwan da suka rubuta zuwa yanzu akwai wani yao mai shekaru 11, wanda shi ma zai samu kyauta.

3616357


captcha