IQNA

Taron Kasashe 15 Mai Taken Taratil Sajjadiyya

21:03 - July 18, 2017
Lambar Labari: 3481713
Bangaren kasa da kasa, kasashe 15 za su halarci taro mai taken taratil Sajjadiyya domin yin dubi a kan wasu bangarori da suka shafi rayuwar limamin shiriya na hudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ana shirin gudanar da wani babban taro a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin karbala a kan Imam Sajjad (AS) tare da halartar baki daga kasashen duniya.

Jamaluddin Sharistani daya daga cikin waanda suka shirya gudanar da wannan zaman taro ya bayyana cewa, daga cikin kasashen da za su halarci taro a kwai: Ingila, Faransa, Amurka, Turkiya, Bangaladesh, India, Ghana, Singapore, Ukraine, Malaysia, Morocco, Aljeriya, Libya, Syria, da kuma Tunisia.

Wannan taro dai zai kunshi abubuwa da dama da suka hada jawabai, da kuma baje kolin wasu abubuwa da suka danganci Imam sajjad (AS) gami da littafai 16 da suka shafi tariinsa da rayuwarsa mai albarka.

Za a gudanar da taron ne a tsakanin manyan hubbarori biyu da suke birnin mai alfarma.

Abin tuni a nan shi ne a shekarar da ta gabata ma an gudanar da wannan taro karo na uku, tare da halartar baki daga kasashen Lebanon, Faransa, Tunisia, Masr, Iraki, Syria, Jordan da kuma Iran.

3620265


captcha