Wannan taro dai ya nuna yadda dukaknin bangarorin suka hadu a kan abu guda, shi ne zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu addininsu da mabiya wadannan addinai da aka safkar daga sama.
Sauran mabiya addinan sun zabi su taru a masallaci ne kasantuwar musulmi ne suke fuskantar matsala ta zamantakewa a tsakanin al'ummomin kasar, musamman sakamakon ayyukan ta'addanci da suka addabi duniya a halin yanzu.
Koa cikin kwanakin baya-bayan nan an yi ta kai bara a kan msuulmi da masallatai da cibiyoyin addinia cikin biranan kasar Birtaniya, bisa hujjar daukar fansa a kan musulmi dangane da ayyukan ta'addanci da wasu suke aikatawa da sunan musulunci.