IQNA

Taron Zagayowar Shahasar Imam Sadiq (AS) A Kasashen Turai

23:30 - July 20, 2017
Lambar Labari: 3481717
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da tarukan zagayowar lokacin shahadar Imam Sadiq (AS) a kasashen turai turai daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyoyin muslunci a Ingila da Hamburg da kuma Vienna tun a daren jiya ne uska fara gudanar da taruka na tunawa da shahadar Imam Sadiq (AS).

A cibiyar muslunci da ke kasar Bitaniya an gudanar da irin wanann taruka, inda Hojjatol Islam Borhan ya gabatar da jawabi dangane da matsayin wannan limami daga cikin limaman shirya masu tsarki na iyalan gidan manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Babban abin da irin wadannan taruka suka mayar da hankali a kansu dai shi ne, tunatar da jama'a matsayin wadannan bayin Allah, da kuma yin koyi da abin da suka yi da wanda suka bayar da umarni, da nisantar haninsu, domin kuwa suna wakiltar manzon Allah, wanda hakan ke nufin cewa su ne wakiltar addinin Allah bayan manzo.

Bayan nan kuma an gudanar da wani taron makamancin hakan a birnin Vienna na, a cibiyar Imam Ali (AS) cibiyar da kan dauki nauyin shirya tarukan addini da kuma raya munasabat na tunawa da hahihuwa ko shahadar wani daga cikin limaman shiriya na gidan manzo.

3621077


captcha