IQNA

Kace Na Ce Dangane Da Buga Kur’ani Mai Launi

23:33 - July 20, 2017
Lambar Labari: 3481718
Bangaren kasa da kasa, buga kwafin kur’ani mai tsarki da launuka daban-daban ya jawo tayar da jijiyoyin wuya a wasu kasashen larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai alkon news cewa, sakamakon buga kur’ani mai lanuka a wasu daga cikin kasashen larabawa hakan ya jawo cece ku ce.

Cibiyar Azhar dai ita ce ta fara hana buga irin wannan nauin kur’ania cikin kasar Masar, inda aka fi buga shi da kuma sayar da shi, kafin daga bisani wasu kasashe su bi sahun wannan mataki.

An fi sayar da wannan kr’ani dai a cikin birnin Alkahira babban birnin kasar Masar inda mutane sukan sayi wannan kr’ani domin tsaraba ko kuma bayar da kyauta ta musamman ga abokai, musamman ma mata daga cikinsu.

A kasar Lebaonon buga wani kur’ani mai launi ya jawo cece ku ce a cikin kasar, inda wasu ke ganin cewa hakan bai kamata ba, yayin da wasu ke ganin cewa babu wani laifi dangane da hakan, domin kuwa babu wani nassi na shari’a da hana yin hakan, kuma babu aibu a zahiri tare da shi.

Wannan dais hi ne karon farko da ake buga irin wannan kur’ani mai launia cikin kasar Lebanon, wanda kuma ya samu karbuwa musammana wajen yara da kuma mata, kasantuwar yana da shafuka masu launi da ke ban sha’awa gare su.

3621167


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha