IQNA

Palastinawa Na Yin Salla A Wajen Masallacin Aqsa

20:35 - July 21, 2017
Lambar Labari: 3481722
Bangaren kasa da kasa, Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus domin hana palasdinawa Isa masallacin kudus.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin i24news cewa, sojojin yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus mako daya bayan hana palasdinawa yin salla a masallacin kudus mai alfarma

Tun da safiyar yau ne sojojin yahudawan su ka kafa shinge na karfe a kofar Babul Asbat ta masallacin kudus, kamar kuma yadda su ka mamaye duk wasu hanyoyin da su ke isa zuwa ga masallacin.

Rahotanni daga kudus sun cewa; 'yan sahayoniyar sun girke sojoji dubu sha biyar a cikin birnin na Kudus.

Dubban palasdinawa da su ka ki amincewa da su bi ta cikin kofar bincike da 'yan sahayoniyar su ka kafa a bakin masallacin kudus.

A wasu sassa-sassa daban-daban na palasdinu an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin sahayoniya.

3621255


captcha