IQNA

An Nuna Kur'ani Mai Nauyin Kilogram 154 A Madina

22:53 - July 22, 2017
Lambar Labari: 3481724
Bangaren kasa da kasa,a wani baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kusa da harami da kuma masallacin manzon Allah a Madina an nuna wani rubutaccen kur'ani mai nauyin kilogram 154.

Kamfanin dilancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na alfajr cewa, Hamza Abdulkarim, mai kula da baje kolin kur'ani a kusa da haramin manzon Allah a Madina ya bayyana cewa, Gholam Muhyiddin shi ne ya rubuta wannan kur'ani tun kimanin shekaru 200 da suka gabata a kasar Afghanistan.

Ya ci gaba da cewa, wannan kur'ani yana da nauyin kilogram 154 hakan na kuma tsawonsa ya kai mita daya da rabi, kamar yadda kuma fadinsa ya kai muta daya.

Abdulkarim ya kara da cewa, an ubuta wannan kur'ani mai tsarki ne a kan fatun barewa, kuma an gayyaci wasu masana kan harkokin tarihi sun bayyana ra'ayinsu dangane da wannan kur'ani, inda suka tabbatar da cewa hakika an yi amfani da fasaha a wurin rubutunsa, haka nan kuma a karshen kowane shafi ana yin karin haske da rubutun farisanci.

Haka nan kuma wasu daga cikin kwafin kur'anan da aka baje wannan wuri akwai wanda Hafez Usman ya rubuta, bayan ya kai shafi na 106 yana cikin na 107 ne ya rasu.

Haka nan kuma ana gudanar da wanan baje koli ne a ckin dakuna 12, kamar yadda kuma masu tarjama a cikin harsuna daban-daban sun halarci wurin, da suka da turancin Ingilishi, faransanci, Farisanci, Urdu, Turkanci, Indnesia da kuma Pashtu.

3621250


An Nuna Kur'ani Mai Nauyin Kilogram 154 A Madina

An Nuna Kur'ani Mai Nauyin Kilogram 154 A Madina
captcha