IQNA

An Kafa Wani Allo Na Kira Ga Muslunci A Chicago

22:57 - July 22, 2017
1
Lambar Labari: 3481725
Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar musulmi mai suna Gain Peace ta bullo da wata sabuwar hanya ta yin kira zuwa ga sanin hakikanin addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin USA Today cewa, wannan cbiya ta musulmi ta bullo da hanyar saka bayanai a kan muslunci a kan manyan alluna da jama'a suke karantawa.

Abin da ta fara yi shi ne yin kira ga mutane da su nemi littafin da aka aka rubuta akan tarihin rayuwar manzon Allah annabi Muhammad (SAW) domin karantawa da kuma sanin hakikanin rayuwarsa.

Babbar manufar hakan ita ce kalubaantar hanyoyin da masu kyamar muslucni ke bi domin bata sunan addinin muslunci ta hanyar jingina ayyukan ta'addanci ga wannan adini, tare da kiran duk wani musulmi dan ta'adda.

Yanzu haka wannan salo ya fara samun karbuwa a wajen Amurkawa mazauna wannan yanki, inda suke neman littafin tarihin manzon Allah wada musulmi suka rubuta da kansu, maimaon dpgaro da littafan da aka rubuta akan musulmi.

Matsalar kyamar musulmia kasar Aurka dai ta yi kamari ne tun bayan da shugaban kasar da ke mulki a halin yanzu ya karbi ragamar shugabanci watanni shida da suka gabata.

3621475


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
YUNUSA ABUKAR MAIKUJERI
0
0
IQNA MUNA GODIYA DALABARAN gaskiya danake samudaga ga reku alla yataimakemu
captcha