Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nkalto daga shafin yada labarai na tap cewa, al'ummar Tunisa suna gudanar da jerin gwano a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia domin la'antar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da cin zarafin musulmin Palastinu da kuma keta alfamar wurare masu tsarki.
Wannan zanga-zanga wadda ta samu halartar dubban al'ummar kasar ta Tunisia ta mayar da hankali ne kan yadda gwamnatocin kasashen larabawa da sarakunansu suka yi gum da bakunansu a kan abin da yake faruwa a kan al'ummar palastinu da kuma masallaci mai alfarma.
Baya ga birnnin Tunis an gudanar da rin wanan babban jerin gwano a wasu biranan na kasar Tunisia a jiya, inda ake la'anatar gwamnatin yahudawan Isara'ila dangane da cin zarafin musulmi da ake yi a birnin Quds.
Tun a cikin shekara ta 1979 ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta kwace iko da birnin Quds a hukumance, tare da mayar da masallacin Aqsa ai alfarm a matsayin wani da ke krkashin ikonsu, za su iya hana yin salla a cikinsa a duk lokacin da suka ga dama.