IQNA

Kira Zuwa Ga Kariya Ga Masallacin Adsa A Birane 16 Na Birtaniya

23:16 - July 24, 2017
Lambar Labari: 3481731
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke fafutukar kare hakkokin Palastinawa a kasar Birtaniya ta yi kira zuwa ga gudanar da taruka a birane 16 na kasar domin taimakon al’ummar birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middleeastmonitor cewa, cibiyar kare hakkokin Palastine da ke da mazauni a kasar ta Birtaniya, ta bukaci jama’a a biranane 16 na kasar da suka hada Bradford, Manchester, New Castle, Lester, Country, Glasco su gudanar da tarukan nunagoyon baya ga al’ummar Palastine.

An kafa wannan kungiya ne tun 1997 inda take gudanar da taruka da waye kan jama’a kan halin da al’ummar palastinu suke ciki, dangane da zalunci da danniya da kuma cin zarafin da suke fuskanta daga yahudawan Isra’ila.

Shi ma a nasa bangaren Paparoma Francis ya yi kira da a gudanar da taron tattaunawa dangane da halin da birnin Quds yake ciki domin a samu mafita da kuma zaman lafiya.

Kamar yadda a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ma kasashen Masar, Sweden da kuma Faransa, sun gabar da bukatar neman a gudanar da zaman gaggawa domin tattauna halin da ake cikia Quds da kawo karshen killacewar da Isra’ila take yi wa masalalcin Aqsa.

3622481


captcha