IQNA

Mutane Da Dama Ne Suka Rasa Rayukansu A Wani Harin Bam A Kabul

23:23 - July 24, 2017
Lambar Labari: 3481733
Bangaren kasa da kasa, wani harin ta’addanci a yankin mazauna mabiya mazhabar shi’a a Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar jama’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, rahotanni daga kasar Afghanistan sun tabbatar da mutuwar mutane aklla talatin da biyar a wani harin da ak akai da wata mota da aka shakare da bama-bamai a cikin birnin Kabul fadar mulkin kasar.

an tayar da motar da shakare da bama-baman ne a cikin wata unguwa ta mabiya mazhabar shi'a a cikin na Kabul a safiyar yau, inda ma'aikatar harkokin cikin kasar ta Afghanistan ta ce mutane talatin da biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu kuma suka samu raunuka.

Rahoton ya ce dukkanin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne, da suka hada da daliban jami'a da suke kan hanyarsu ta zuwa jami'a domin rubuta jarabawa.

Kungiyar Taliban ta daukialhakin kai harin, kamar yadda kungiyar ta Taliban ta ‘yan ta’adda masu dauke da akidawar wahabiyanci da ke kafirta sauran al’ummar musulmi suka saba, sukan kai irin wadannan hare-hare a kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.

3622385


captcha