Wannan taro dai ya gudana ne domin yin bita dangane da abubuwan da suke jawo tsatsauran ra'ayi a cikin addini wanda har ya kan kai wasu ga aikata muggan ayyuka da sunan addini, duk da cewa an fi saurin danganta wasu mabiya addinin muslunci da hakan, amma akwai wasu daga cikin sauran addinai da suke aikata laifuka na ta'addanci da sunan addini.
Musulmin da suka halarci wurin dai sun yi karin haske ga mahalarta wurin da cewa, addinin muslucni addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai da ma al'adu, kuma masu aikata ta'addanci da sunan muslunci ba suna wakiltar addininmuslunci ko musulmi ba ne.
3622892