IQNA

Farashin Kudin Kujerar Hajjin Bana Ya Yi Tashin Gwabron Zabi A Masar

17:49 - July 25, 2017
Lambar Labari: 3481735
Bangaren kasa kasa, al'ummar kasar Masar suna kokawa matuka dangane da karin farashin kujerar hajjin bana da hukumar alhazi ta kasar ta yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,

Shafin yada labarai na Almisrawi ya bayar da rahoton cewa, farashin kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar masar ya ninka har sau kusan biyu da rabi idan aka kwatanta da farashin shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce al'ummar kasar suna ta kokawa matuka kan wannan lamari, inda tuni wakilan jama'a  amajalisar dokokin kasar siuka gabatar da wannan magana da nufin neman yin sassaucin a kan lamarin.

Sai dai a nasa bangaren babban daraktan hukumar alhazai ta kasar Aiman Sami ya bayyana cewa, ba da son ransu ne hakan ke faruwa ba, domin kuwa mahukuntan Saudiyya ne suka kara musu yawan kudaden haraji da suke karba daga kamfanonin jigilar alhazai, kamar yadda hatta kudaden biza sun ninka kusan sau uku, inda ya ce wannan lamari yana a matsayin wata annoba.

3621951



captcha