IQNA

Sayyid Nasrallah:

An Samu Nasara A Cikin Sa'oi 48 Na Farkon Farmaki

17:26 - July 27, 2017
Lambar Labari: 3481740
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid hassan Nasrullah bayyana cewa acikin sa'oin farko na fara kaddamar da farmaki kan yan ta'adda aka samu nasara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar dakarun kungiyar sun kusa kwato dukkanin yankunan kasar Labanon da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra suke rike da su tsawon shekaru, yana mai jinjinawa irin namijin kokarin da dakarun kungiyar da sojojin Labanon suka yi wajen cimma wannan nasarar.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a daren jiya Laraba don karin haske dangane da hare-haren da dakarun kungiyar da suke samun goyon bayan sojojin kasar Siriya da Labanon suka kaddamar da nufin fatattakan 'yan kungiyar ta'addancin ta Jabhatun Nusra daga kan iyakokin kasashen biyu inda ya ce a halin yanzu dai dakarun Hizbullah din sun sami nasarar fatattakan 'yan ta'addan gaba daya daga yankin Fleita na kasar Siriya, a bangaren kasar Labanon kuwa saura kadan ya rage a fatattake su gaba daya.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa tun bayan da dakarun kungiyar suka kaddamar da wadannan hare-hare a yankin Jurud Arsal a ranar Juma'ar da ta gabata suke ci gaba da samun nasarori a kan 'yan ta'addan inda ya ce dakarun kungiyar za su ci gaba da kai wadannan hare-hare har sai an cimma manufar fatattakan 'yan ta'addan daga yankin, sai dai ya ce har ya zuwa yanzu kofa a bude take ga 'yan ta'addan da su ajiye makamansu su bar yankin.

A watan Augustan 2014 ne dai 'yan ta'addan kungiyar Jabhatun Nusra din da wasu kungiyoyin 'yan ta'addan suka kwace yankin na Arsal daga hannun sojojin Labanon bayan da suka kashe da kuma sace wasu sojojin su 30, inda suka yi ta amfani da yankin wajen kai hare-haren ta'addanci cikin yankuna daban-daban na kasar Labanon, lamarin da Hizbullah din suka ce ba za su ci gaba da zuba ido kan hakan ba.

3623574


captcha