Rahoton ya ce mutane da dama sun jikkata, yayin da waus suke cikin mawuyacin hali, sakamakon shakar isakar gas da jami'an tsaron suke fesawa wanda ke dauke lumfashi, musamman ma ga masu matsaloli na musamman da suka shafi lumfashi.
Yanzu haka mahukuntan masarautar Al Saud da ke rike da madafun iko a kasar suna shirin fille kawunan wasu fararen hula sha hudu daga wannan yanki, bisa zarginsu da shiga jerin gwanon nuna rashin gamsuwa da salon mulkin Al Saud.
Al'ummar yankin gabashin Saudiyya dai mabiya mazhabar shi'a ne, kuma suna yin korafi ne dangane da yadda aka mayar da su saniyar ware, tare da haramta musu hakkokinsu na 'yan kasa, duk kuwa da cewa dukkanin arzikin man fetur da iskar da tattalin arzikin kasar ya dogara da shi, ana fitar da su ne daga yankinsu.