IQNA

Horar Da Malaman Kur'ani A Senegal Tare Da Halartar Malami Daga Iran

21:02 - July 30, 2017
Lambar Labari: 3481751
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na horar da malaman kur'ani a kasar Senegal karkashin jagorancin ofishin al'adun muslunci na Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, bangaren hulda da jama'a na ciyar yada la'dun muslunci na jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayar da rahoton cewa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga malaman kur'ani a Senegal.

Shirin zai gudana ne a garin Tuba babbar cibiyar mabiya darikar Muridiyyah a kasar ta Senegal, a karkashin kulawar cibiyar kula da al'adun muslunci, wanda ofishinta da ke Senegal zai dauki nauyin shirin.

Wannan dais hi ne karon farko da za a gudanar da wannan horo a wajen birnin Dakar wanda cibiyar take daukar nauyinsa, inda Majid Zakilou fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Iran zai kasance daga cikin malamai masu bayar da horon.

3624130


captcha