IQNA

Shirin Koyar Kur'ani A Masallacin Azhar Ya Samu Karuwa

22:58 - July 31, 2017
Lambar Labari: 3481754
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da washiri na koyar da kur'ani da hakan ya hada da harda dama wasu ilmomin na daban a masallacin cibiyar Azhar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na fath-news.com cewa, baya ga koyar da karatun kur'ani da salo na musamman na karatu, ana koyar da hardar kur'ani mai tsarkia zaman.

Wannan shiri dai ya samu karbuwa fiye da yadda aka yi zato daga bangarorin daliban jami'ar da kuma malamai gami da jama'ar gari masu bukatar koyon karatun kur'ani na tangimi a masallacin cibiyar ta Azhar.

Baya ga ilmomin karatu da hardar kur'ani mai tsari, shirin ya hada da koyar da wasu ilmomin da suka da fikihu, hadisi, tafsiri da kuka akida gami da ilmin larabci da ya hada da sarf da nahawu ga daliba 'yan kasashen ketare.

3624761


captcha