IQNA

Wani Matshi A Sudan Ya Hardace Juzu’i 22 Cikin kankanin Lokaci

23:53 - August 04, 2017
Lambar Labari: 3481766
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Usman Muhammad Umar wani matashi mai nakasa a kasar Sudan a garin Snar ya hardace juzu’i 22 na kur’ani mai tsarki a cikin gajeren lokacin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Khartum Post cewa, wannan yaro Ahmad Usman Muhammad Umar mai shekaru 11 a duniya yana rayuwa ne a garin Sinar.

Sheikh Muhammad Shasuddin shugaban bangaren kula da harkokin kur’ani a lardin Sinar ya bayyana cewa, duk da matsalar da yake fama da ita ta nakasa a jikinsa, amma kuma a lokaci guda Allah yah ore masa kwalwar gane karatu a cikin karamin lokaci, kuma yana da saurin hardace duk abin da ya ji.

Amirah Muhammad Hashim Muhammad ahmad wadda ita ce mahaifiyar wannan yaro ta bayyana cewa, bisa la’akari da matsalolin da yake da su, hakan ya sanya baya iya halartar wata cibiya domin hardar kur, amma daga bisani kuma ta lura cewa yana da kaifin basira, saboda haka sai ta fara koya masa karatun kur’ani da harda da kanta.

3626606


captcha