IQNA

Yaro Dan Shekaru 6 Mahardacin Kur’ani A Najeriya: Ina Son zama Likita

23:32 - August 06, 2017
Lambar Labari: 3481773
Bangaren kasa da kasa, wani yaro dan shekaru 6 da haihuwa da ya hardace dukkanin kur’ani mai tsarki a Najeriya, ya bayyana cewa yana son zama likta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na naij cewa, Salim Abdulkarim dan shekaru 6 da haihuwa ya fara hardar kur’ani ne daga cikin watan mayun 2016 ya kuma kammala zuwa watan mayun 2017.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai ya bayyana cewa; babban burinsa shi ne ya zama likita domin ya taimaka mutanen kasarsa, musamman ma marassa karfi daga cikinsu da suke butar taimako.

Malam Hamza Jibril shi ne shugaban makarantar da wannan yaro tyake karatu, ya bayyan acewa farfesa Abdulkarim Ahmad shi ne mahaifin wannan yaro, ya kuma kawo shi domin yin karatun kur’ani da harda.

Malamin ya ce sun koyar da wannan yaro a cikin shekara guda, duk kuwa da cewa dai mahaifinsa ne ya matsa kuma y adage a kan hakan, inda hatta hutun karshen mako ba abarin Salim yaje gida, a kullum yana cikin karatu.

Daga karshe yace Salim zai halarci gasar kur’ani a kasar saudiyya, duk kwa da cewa kafin shi wasu daga cikin daliban kur’ani na wannan makaranta sun wakilci a najeriya a gasar kr’ani ta kasa da kasa a kasashen duniya daban-daban.

3627101


captcha