IQNA

Bayanin Surat Hamd A Wani Taron Jagororin Addinai A Amurka

23:56 - August 08, 2017
Lambar Labari: 3481779
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na mabiya addinai a birnin Vioming na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai Vioming News ya bayar da rahoton cewa, kimanin mutane 200 ne suka halarci wannan zama, da suka hada da jagoron mabiya addinan kiristanci da muslucni da kuma yahudanci.

Muhammad saleh wanda shi ne wakilin musulmi a wannan taro ya yi ishara da ayoyi na 6 da kuma 7 a cikin surat Hamd, wadanda suke a matsayin addu’a ta neman shiriya daga Allah madaukakin sarki, inda kuma aka tarjama wadannan ayoyi da harsuna daban-daban a wannan wurin taro domin kowa ya fahimci ma’anarsu.

Warn Murffy shi ne shugaban majami’ar mabiya addinin kirista ta wannan birnin ya bayyana cewa, wannan taro ana gudanar da shi ne domin cika shekaru dari da hamsin da kafuwar birnin, wanda yana daya daga cikin biranan kasar da mabiya addinai suke da fahimtar juna.

Culter Andrrson shi ma daya ne daga cikin jagororin mabiya addinin kirista, ya bayyana gamsuwarsa matuka a kan yadda dukkanin mabiya addinai suka taru wuri guda suna masu fahimta juna da girmama addinansu.

3628021


captcha