IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani A Kan Kur'ani A Masar

23:40 - August 11, 2017
Lambar Labari: 3481787
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan rubutun larabci a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, Faisal Alhafyan babban daraktan cibiyar incike akan rubutun larabci ya bayyana cewa, za agudanar da wannan zaman taro nea yau a birin Alkahira.

Ya ce ko shakka babu wannan shi ne karon farko da za agudanar da wannan zaman taro a cikin wanann shekara ta 2017 kuma yana fatan hakan ya zama digon dan ba, domin ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka ashekaru masu uwa.

Babbar manufar wannan taro dai ita ce yin yin dubi a kan rubutun larabci, wanda da shi ne aka rubuta kur'ani mai tsarki, da kuma irin sauye-sauyen da ya samu a cikin tsawon shekaru fiye da dubu daya da dari hudu da suka gabata.

Haruffan larabci da ake yin amfani da su a halin yanzu wajen rubutun kur'ani ko kuma wani matani na larabci suna da dan bambanci da haruffan da aka yi amfani da su tun lokacin saukar kur'ani mai tsarki, inda wadannan haruffa suka ga canji da kuma kare-kare.

Misalin hakan shi ne digo a kan harafi ko kasan harafi da ake amfani da su a halin yanzu, wanda a lokacin saukar kur'ani ba a yin amfani da su, kamar wasulla wadabda duk daga baya ne aka samar da su domin samun sauki wajen karatu da kuma saurin nriskar ma'anar da ake nufi ba tare da kure ko shakku ba.

3628431


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna juna
captcha